<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>154</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Yesu yana so ya zauna
 Cikin zuciyar mutane.
 Shi ya ɗauke laifofinka
 Ranka kuma ya ke so.

[V2]
 KORUS
 Yesu yana bakin ƙofa,
 Sai ka ji maganarsa,
 Buɗe ƙofar zuciyarka
 Yi wa Yesu maraba.

[V3]
 2) Akwai dama domin wasa
 Akwai damar aiki kuwa.
 Babu wuri domin Yesu
 Cikin zuciyar mutane.
 Korus

[V4]
 3) Yau ne lokacin alheri,
 Akwai ceto dominmu.
 Kila gobe babu dama,
 Gobe fa ba tamu ba.
 Korus

[V5]
 4) Kwanakinmu kamar iska
 Suna wucewa da sauri.
 Sai ka tuba, karƃi Yesu
 Kamin ranar fushinsa.
 Korus</lyrics>
<title>Yesu Yana So Ya Zauna LW154</title>
</song>